Janar Yahaya, ya maye gurbin marigayi Laftanar Janar Ibrahim Attahiru, wanda ya ya rasu a makon da ya gabata a wani hatsarin jirgin sama tare da wasu sojoji 10.
Tun bayan wannan nadi, bayanai da suka shafi tarihin sabon shugaban rundunar sojin kasa na Najeriyar ke ci gaba da fitowa.
A ranar Alhamis, Fadar Shugaba Muhammadu Buhari ta saki takardar da ke dauke da takaitaccen tarihin rayuwar Janar Yahaya, wadanda suka bayanan ranar haihuwarsa, inda aka haife shi, mukamai da ya rike da lambobin yabo da ya samu a ciki da wajen Najeriya.
Karin bayani akan: Janar Yahaya, Laftanar Janar Ibrahim Attahiru, Garba Shehu, Boko Haram, Abubakar Shekau, Shugaba Muhammadu Buhari, Nigeria, da Najeriya.
Daga cikin bayanan har ila yau akwai harsuna hudu da sabon babban hafsan ya kware akansu, kamar yadda fadar shugaban kasar ta fitar ta hannun kakakin Buhari Malam Garba Shehu.
Harsunan sun hada da “Ingilishi, Hausa, Larabci da kuma Spaniyanci.” Kamar yadda takardun Janar Yahaya suka nuna, wanda Garba Shehu ya wallafa a Twitter.
Sanarwar ta kara da cewa, yana kuma iya rubutu da wadannan harsuna har da Spaniyancin.
An haifi sabon babban hafsan hafsoshin sojojin Najeriya a ranar 5 ga watan Janairun 1966, a Sifawa dake yankin karamar hukumar Bodinga dake Jihar Sokoto a arewa maso yammacin Najeriya.