Dan wasan Gaba na kungiyar kwallon kafa ta Tottenham Harry Kane, ya kafa tarihi a bangaren jefa kwallaye a gasar firimiya lig ta kasar Ingila bisa tsarin kalandar shekara shekara.
A yanzu haka Harry Kane, ya Zurara kwallaye 39 a shekara ta 2017 a wasannin firimiya lig inda ya haura kan tsohon dan wasan Blackburn Alan Shearer, wanda ya jefa kwallaye 36 a shekarar 1995.
Harry Kane, ya samu wannan nasara ne a wasan da kungiyarsa ta Tottenham ta yi da Southampton, inda ta lallasa ta daci 5-2 a gasar Firimiya lig, mako na ashirin, dan wasan ya jefa kwallaye uku a cikin biyar da Tottenham ta samu.
Hakan yasa Harry Kane, mai shekaru 24 da haihuwa ya zamo dan wasan da yake kan gaba a yankin Nahiyar Turai wajan zuba kwallaye a raga idan an hada da kwallayen da yaci wa kasarsa ta Ingila guda 17, jimilar kwallayensa 56 kenan a shekarar 2017.
Sai Lional Messi, ke biye da shi da kwallaye 54, Lewandowski da kwallaye 53 sai Cristiano Ronaldo 53, Cavani 53.
Your browser doesn’t support HTML5