Ministan matasa, wasannin motsa jikin da al'adu na kasar Nijar, Malam Kasim Mukhtar, ya kaddamar da buda shagulgulan kokowar gargajiya karo na talatin da tara, (39) a Damagaram, inda ‘yan kokowa na jihojin jamhuriyar Nijar, za su kara har tsawon kwanaki goma don samun zakaran da zai dauko takobi.
Mauduin da aka dauka a bana shine gudurmawar matasa a tsarin farfado da kasar Nijar, wanda al’adu na taka mahimmin rawa a cikinsa.
Yahaya Muhammad shugaban kwamitin tsara kokowar ya ce a bana jama’a zasu ga kokowa mai ban sha’awa kuma cikin kyakkyawan tsaro da kuma wani sabon tsari na saka kokowar nakasassu a ciki a bana domin suma a dama dasu.
Ya kara da cewa za a tabbatar da ganin cewa an magance kura kuran da suka faru a baya domin cigaban kokowa a kasar Nijar.
A kokowar ta yau Dosso ta kara da Diffa Maradi da Tillaberi, Dosso ta tashi da kaye shida Diffa kaye uku mutuwar kasko daya.
Facebook Forum