A yayinda da ake dab da bude kofar cinikaiyar ‘yan wasan kwallon kafa na duniya a watan Janairu 2018, Kocin kungiyar Tottenham, Pochettino ya ce kulob din ya shirya wajan sayo ‘yan wasanni a watan Janairu mai zuwa irin su Ross Barkley, na Everton, Luke Shaw na Manchester united.
Pep Guardiola yana da shi'awar ganin ya dauko dan wasan Tsakiya na Shakhtar Donestk, mai suna Fred. Arsenal ta jera sahu daya da Manchester united, da Chelsea, wajan zawarcin dan wasan gefe na Bayern Leverkusen Leon Bailey.
Westham tana zawarcin dan wasan tsakiya daga Bournemouth Harry Arter, mai shekaru 27 da haihuwa, Manchester United, yana shirye shiryen dauko dan wasan baya na gefen hagu daga Fulham mai suna Ryan Sessegno, dan shekaru 17 da haihuwa akan kudi fam miliyan £25.
Shugaban kungiyar Kwallon kafa ta Monaco, ya ce basa tunanin sayarda Thomas Lemar, a watan Janairu, Su kuwa Kungiyoyi irinsu Arsenal, Liverpool da Chelsea, sun kwallafa ransu wajan ganin sun dauko dan wasan a watan gobe.
Sam Allardyce, yana shi'awar ganin ya dauko Steven N'zonzi, daga Sevilla zuwa Everton, Steven mai shekaru 29 a duniya ya buga wasa a kar kashin kungiyar Allardyce, a lokacin yana Blackburn.
Arsenal, ta maida hankalinta wajan ganin ta haura kan Liverpool, domin sayen dan wasan gefe dan kasar Holland, Alessio Da Cruz, wanda yake fafata wasanni a kungiyar Novara, a kasar Itali.
Paris Saint-Germain, tana zawarcin dan wasan tsakiya na Aljazira, Lassana Diarra, Manchester city, tana zawarcin dan wasan baya na AC Milan, Leonardo Bonucci.
Real Betis, tana neman dan wasan gaba na PSG, Lucas Moura a matsayin aro, Juventus na zawarcin Aaron mai tsaron baya na kungiyar Espanyol, Manchester city tana zawarcin Segiou Busquets daga Barcelona akan kudi fam miliyan £56.
Roma tana zawarcin dan wasan tsakiya na Inter Milan Joao Mario a matsayin aro, itama Inter Milan na bukatar dauko dan wasan baya na Roma Emerson, da ya dawo kungiyar a matsayin aro.
Facebook Forum