‘Yar takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar Democrat Kamala Harris ta yi kira ga Amurkawa da su “daina dora wa juna laifi” yayin da take kokarin disar da kalaman da Shugaba Joe Biden ya fada game da magoya bayan Donald Trump da inda ya kwatanta su a matsayin “shara.”
Shugaba Biden dai ya ce baa bin da yake nufi ba kenan duk da cewa masu lura da al’amura sun ce ya makara.
Harris ta gabatar da jawabin nata a Raleigh, North Carolina, Harrisburg, Pennsylvania, da Madison, Wisconsin, a wani gagarumin rangadi da ta yi a jihohin da za a gwabza sosai a zaben, a makon karshe kafin ranar zabe.
Ta jaddada hadin kai da fahimtar juna, tana mai fadada kan jawabin nata na karshe da ta yi ranar Talata a birnin Washington, inda ta bayyana abin da tawagarta ta kira “hudubar karshe” na yakin neman zabenta.
Harris ta cewa manema labarai, “zan wakilci duk Amurkawa, har da wadanda ba za su zabe ni ba.”
A halin da ake ciki, Fadar White House ta yi maza-maza ta yi karin haske kan kalaman na Biden tana mai nuni da cewa martani ne ya yi ga kalaman mukarraban Trump.
Sakatariyar yada labarai Karine Jean-Pierre ta fadawa manema labarai cewa Biden ba ya kallon magoya bayan Trump ko wani a matsayin shara.