Tuni dai aka fara shigo da shanu daga kasashen ketare inda harkokin suka fara komawa kamar da, koda yake dillalan Shanu na kokawa da cewa jami'an tsaro na musguna musu wajen karbar na goro.
A cewar wasu yan kasuwa yanzu haka harkoki sun fara komawa kamar yadda suke a baya, abin da kuma ya rage musu harka a kasuwar shine maganar tashin Dala, domin ta rage yawan harkar saye da sayarwa.
To sai dai kuma yayin da lamura suka fara daidai ta yanzu haka wata matsala da fataken Shanun ke fuskanta itace ta tsangwama da kuma karbar na goro da suke zargin ana karba a hannunsu. Wakilin Muryar Amurka Ibrahim Abudulaziz, yayi kokarin jin ta bakin jami’an tsaro abin ya ci tura domin kowa yayi shiru da bakinsa.
Domin karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5