A lokacin mika wannan yarinya ga iyayenta a hedkwatar yan Sanda dake birnin Abuja, kakakin rundunar yan Sandan Najeriyar Olabisi Kolawole tace, “Abune tabbatattce hukumar Shari’a ta jihar Kano, da ofishin Sifeta Janal na yan Sandan Najeriya shiya ta daya dake Kano, tuni sun samar da masalaha ga wannan batu. Yayin da wannan yarinyar ke hannun hukuma ne ake ganin kamar wani abu ne daban, harkar dai ta kunshi bin matakai masu yawa.”
Mahaifiyar wannan yarinya dai tace tana yabawa yan Najeriya, bisa yadda sukayi tsayin daka har ta sami diyarta. Inda tace tana godewa kowa da kowa, kuma yanzu ta sami dayarta kuma zasu koma gida.
Wani dan rajin kare hakkin bil Adama a Najeriya, Kwamrad Abubakar Abdussalam, ya nuna damuwa bisa yadda takwarorinsa masu fafutuka suka yi ta karin gishiri dan gane da wannan batu na Ese Orure. Saboda tun kafin maganar ta fito an dauki yarinyar an kai ta gaban mai martaba sarkin Kano, wanda bai goyi bayan maganar ba saboda yarinyar bata mallaki hankalin kanta ba.
Domin karin bayani.