Bamabaman sun fada ne akan sansanin da aka tanadawa 'yan gudun hijira kusa da iyaka da kasar Turkiya.
Akalla mutane 30 ne suka rasa rayukansu a sansanin Kamouna kusa da Samada a yankin Idlib dake arewacin Syria kuma mutane da dama sun jikata sanadiyar hare-haren ta jiragen sama kamar yadda kungiyar dake hamayya da shugaba Assad ta sanar.
Hotunan da kungiyar ta nuna an ga wuraren da bamabaman suka rugurguza. Mai magana da yawun shugaban Amurka Barack Obama, Josh Earnest yace mutanen da aka kaiwa hari sun riga sun tagayyara saboda rashin muhallansu ya kaisu sansanin 'yan gudun hijira sai gashi kuma ana jefa masu bamabamai. Yace babu hujjar yin hakan.
Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka tace tana bukatar cikakken bayani akan lamarin tare da cewa ma'aikatar ta ga rahoton da yace gwamnatin kasar ce ta kai hare-haren.