Harin Rundunar Sojin Sama Ya Hallaka ‘Yan Ta’adda A Borno

Bangaren sojin sama na aikin wanzar da zaman lafiya na “Operation Hadin Kai” ya hallaka dimbin ‘yan ta’adda a yankuna 2 na garin Bula Marwa dake jihar Borno.

Rundunar sojin saman Najeriya (NAF) ce ta bayyana hakan a sanarwar da ta fitar a jiya Litinin, inda tace an gudanar da samamen ne a ranar 25 ga watan Oktoban da muke ciki.

Daraktan yada labaran rundunar sojin saman, Air Commodore Olusola Akinboyewa, yace an gano cewa garin Bula Marwa ya zama matattarar mayakan Boko Haram da suka yi kwaurin suna, don haka bayanan sirri da sa idanu suka kara tabbatar da karuwar ayyukan ‘yan ta’adda a yankin.

Akinboyewa yace, an tura jiragen saman yaki zuwa yankin domin gudanar da samame ta sama bayan da bayanan da aka tattara suka tabbatar da kwararowar ‘yan ta’adda zuwa yankin.

Ya cigaba da cewar an sake nadar bayanai a wannan rana, wadanda suka gano wani gungun ‘yan ta’addar a tattare a karkashin wata bishiya a wata matattara ta daban.

A cewarsa, rundunar sojin saman ta kaddamar da harin a daidai wurin, inda tayi nasarar samu tare da hallaka dimbin ‘yan ta’adda.