Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Boko Haram Sun Kashe Mutane 11 A Borno, Inji Ndume


Boko Haram ta yi ikirarin kakkabo jirgin saman soji
Boko Haram ta yi ikirarin kakkabo jirgin saman soji

Yayin da yake tabbatar da kai hare-haren, Sanata Ali Ndume yace 'yan ta'addar sun kuma kona motocin soja 2 a wani harin kwanton bauna da aka kai kusa da kauyen Kirawa dake kan iyakar jihar.

'Yan ta'addar Boko Haram sun hallaka manoma 11 a kauyukan kan iyakar dake kewayen tsaunukan mandara a karamar hukumar Gwoza ta jihar Borno a makon da ya gabata.

Haka kuma an sace akalla wasu mutanen 15 tare da jikkata wasu da dama a hare-haren 'yan ta'addar.

Yayin da yake tabbatar da kai hare-haren, Sanata Ali Ndume yace 'yan ta'addar sun kuma kona motocin soja 2 a wani harin kwanton bauna da aka kai kusa da kauyen Kirawa dake kan iyakar jihar.

“An samu sabbin hare-haren Boko Haram a yankinmu. An yi rashin sa'a, Gwoza na cikin kananan hukumomin da al'amarin yafi shafa bayan fashewar bam watanni 2 da suka wuce," a cewar Ndume wanda ya kasance tsohon shugaban kwamitin Majalisar Dattawa a kan harkokin soja.

"A makon da ya gabata, Boko Haram suka yiwa manoma kwanton bauna ko kuma suka kai musu hari yayin da suke tsaka da girbin amfanin gonarsu, inda suka kashe 8 a kauyen Ngoshe tare da sace mutane 5 sannan mutum guda ya jikkata."

Sanata Ndume ya godewa jami'an tsaro saboda jajircewarsu saidai ya koka da cewar sojoji basu da kwarin gwiwar yakar ta'addancin Boko Haram.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG