Harin Kunar Bakin Wake Ya Kashe Sojojin Yamal 48

Wurin da aka kai harin kunar bakin wake jiya Lahadi

Bisa alamu kungiyar ISIS tana tsananta hare haren da take kaiwa kasar Yamal duk da cewa tana fama da yaki a kasar Iraqi da yankin kasar Siriya inda aka kusa kakkabeta

Jiya Lahadi wani mai harin kunar bakin wake ya kashe sojojin kasar Yemen arba’in da takwas a birnin Aden mai tashar jiragen ruwa a yayinda manyan ma’aikatan jakadancin kasashen Larabawa dana yammacin duniya suke yin wani taro a kasar Saudi Arabiya domin tattaunawa akan rikicin da ake yi a kasar.

Kungiyar ISIS tayi ikirarin cewa ita keda alhakin kai harin. Tunda farko kungiyar tace ta kai hari makamancin wannan a birnin Aden mako guda daya shige ta kashe akalla sojoji arba’in da biyar da raunana wasu da dama.

Yanzu haka sakataren harkokin wajen Amirka John Kerry yana kasar Saudi Arabiya yana ganawa da sarki Salman tare da wasu Ministocin harkokin wajen wasu kasashe domin yin shawarwari akan yakin da ake yi a kasar Yemen tare da wakilin Majalisar Dinkin Duniya na musamman Ismail Ould Cheikh Ahmed.