Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Houthin Yamal Sun Harba Makamai Masu Linzami da Suka Fadi Kusa da Jirgin Yakin Amurka


Wurin da jiragen yaki suka farma da bamabamai a Yemen.
Wurin da jiragen yaki suka farma da bamabamai a Yemen.

Rundunar Sojin Amurka ta ce an harba wasu Makamai masu linzami har guda biyu daga bangaren da Houthi suke rike da shi a Yemen zuwa inda wani jirgin ruwan Amurka yake a tekun Farisa.

Jami’an sojin sun ce makaman masu linzami da aka harba cikin mintuna 60, sun fada a ruwa jiya Lahadi ba tare da sun taba jirgin yakin Amurka mai suna USS Mason ba.

Kakakin ma'aikatar tsaron Amurka, Kyaftin Jeff Davis, yace babu wanda ya samu rauni, haka ma babu wani abin da ya lalace a jikin jirgin. Mun auna cewar wadannan makamai masu linzami sun fito ne daga yankin dake hannun 'yan Houthi a kasar Yemen in ji shi.

Har yanzu dai babu tabbas a kan ko an auna kai harin ne a kan wannan jirgin ruwan yaki na Amurka.

Wani jami'in tsaron Amurka da ba ya son a fadi sunansa yace jirgin yakin mai suna USS Mason yana amfani da wasu matakan tsaron kai daga makamai, koda yake bai san ko wadannan matakan ne suka sa makaman da aka cilla suka fada cikin ruwa kawai, ko kuma da ma tun farko a ruwan zasu fada ba.

XS
SM
MD
LG