Mutane akalla 10 sun mutu sannan wasu kuma 15 sun samu raunuka, a wani mummunan harin kunar bakin wake da aka kai da mota a Mogadishu, babban birnin kasar Somaliya a yau dinnan Lahadi, a cewar majiyoyin tsaro.
Motar da aka tayar da bama-baman ciki, dama ta na kan wani layi ne na jerin motoci a hanyar Maka Al-Mukarrma, wadda ita ce hanyar da ta fi cika da hada-hada a birnin na Mogadishu, a cewar shaidun gani da ido.
Wani wakilin Sashin Somaliyanci na Muryar Amurka, wanda ya je inda abin ya faru, ya ce motar ta rasa na yi ne saboda cinkoson ababen hawa da kuma tsananin binciken da jami'an tsaro ke yi.
Don haka sai maharin ya tayar da bama-baman da ke jibge cikin motar, inda ya kashe mutane 7 da ke wurin. Wasu mutane 3 zuwa hudu kuma sun mutu daga baya, a cewar Mr. Duniya Muhammad Ali, wani jami'in asibitin "Madina Hospital" da ke birnin.
Akasarin wadanda abin ya rutsa da su masu saye da sayarwa ne, wadanda su ka samu kansu cikin al'amarin bayan fitowarsu daga cikin manyan kantunan .