Tuni dai shugaban Zimbabwe Robert Mugabe,wanda shine kan gaba a jerin shugabannin kasashe mafi yawan shekaru a duniya. Dan shekaru 93 da haifuwa, Shugaba Mugabe yace yana cike da koshin lafiya da zai sa ya sake takara a badi, yayi watsi da kiraye kiraye ya zabi magaji idan har rai yayi halinsa.
Duk da ci gaba da safa da marwa da shugaban yake yi zuwa Singapore domin jinya, yanzu kiraye kirayen ya nada magaji sun karu. Na baya bayan nan cikin masu kirayen ya nada magaji wanda ba'a tsammani tayi haka, itace uwargidansa.
Uwargida Grace Mugabe yar shekaru 52 da haifuwa, ta ambato wannan batu a taron jam'iyyar ZANU-PF mai mulkin kasar reshen mata, inda mahalarta suka dare da sowa.
Ana rade raden cewa uwargidan shugaban tana daga cikin jerin wadanda zasu gaje shi, tareda mataimakin shugaban kasa Emmerson Mnangagwa.
Parfessa Shadrack Gutto na jami'ar Afirka ta kudu, yace uwargidan shugaban kasan tana kokarin ganin mijinta ya zabe ta. Duk da haka yace tayi kuskuren cewa, fadarsa itace karshen magana. Yace haka ne kurum muddin yana raye.
Facebook Forum