Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Daliban Kiwon Lafiya A Jamhuriyar Niger Sun Taimakawa Al’ummomin Damagaran.


Khalifa a hannun uwarsa da ma'aikaciyar asibiti
Khalifa a hannun uwarsa da ma'aikaciyar asibiti

Daliban a jamhuriyar Niger masu koyon aikin likita sun taimaka wa jamaar Damagaran da gwaje-gwajen klafiyar su.

Akan wannan taimako da daliban suka bayar wasu mutane da suka je a binciki lafiyar su, sunyi bayanin irin alfanu da suka samu daga wannan yunkuri. Misali wata mace tayi bayanin cewa sau 3 take zuwa somin samun jinya.

Shi kuma wani mutum yayi bayanin cewa sun ji dadin wannan yunkuri na duba lafiyar su, wanda bai zo ba kuma ya kamata ya canja ra’ayi, yazo a dubi lafiyar sa, tunda kana zaune baka san abinda yake damun ka’’

Haka kuma daya daga cikin wadanda suka ji dadin wannan yunkuri, yace gaskiya an binciki lafiya kuma an basu shawarwari wadanda ya dace a rayuwa mutun ya dan rika kula da lafiyar sa Yace wanna kokari ne me kyau idan ana samu ana haka insha ALLAHU duk wanda bai san yadda zai kula da lafiyar sa , ana bada shawara mai kyau akan abinda ya kamata mutum yayi domin kula da lafiyar sa’

Haka dai mutane suka ci gaba da baiyana gamsuwar su, idan wani yaci gaba da cewa, wannan abu da akayi gaskiya munji dadi tunda wannan zuwa da suka yi na duba lafiyar jamaa yana da kyau, da kudin ka ma wani lokacin zaka je a duba maka ballantana ALLAH ya kawo rahusa kazoo ka samu a kyauta’’

Sani Dan Sallau shine wakilin kungiyar Foausani da take taimakawa wa wadannan daliban da suke karatun likitanci.

Yace, dalibai masu karatu ta fannin likita da taimakon ONG Foursani masu kula da masu cutar sukari suka tsara wannan ranar domin ayi wa mutane gwaji kyauta a san masu cutar Diabetic, domin wasu basu san ma suna da ita ba,wasu kuma suna da ita amma basu kula, yadda a ka tsara wannan aiki nay au mutane zasu san matsayin su game da wannan cutar idan kana da ita akwai inda zaa tur aka kaci gaba da karban magani da kuma kula da kiyaye wa, idan kuma baka da ita kasan matsayin ka kana iya cigaba da rayuwar ba wani matsala’’

Wannan magani da binciken lafiya ana yinsa ne kyauta ba tare da bada ko kwabo ba.

Ga Tamar Abari da Karin bayani 3’16

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:16 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG