Sakamakon wucin gadi ya ce lamarin ya haddasa mutuwar mutane tara cikinsu har da 'yan kunar bakin waken uku, yayin da mutane 35 suka ji rauni. Wata majiyar kiwon lafiya da ta bukaci a saya sunanta tace a ciki akwai mata biyu da namiji guda da suka tada bam din .
Yanzu haka almajirai da malaman da wannan harin ya rusta da su na can kwance a asibitin Diffa domin ci gaba da jiyya.
Shugaban majalisar mashawartan yankin diffa ya tabbatar da faruwar wannan al'amari, ko da yake ya ce har yanzu suna cikin harhada bayanai.
Yankin Diffa na daga cikin yankunan da gwamnatin Nijar ta kafawa dokar ta baci domin murkushe hare haren boko haram. kuma rahotanni na cewa harin kunar bakin waken na jiya, ya sa hukumomi suka dauki tsaurara matakan tsaro a dukka wajejen taron jama'a, musamman a ciki da wajen kasuwar garin Dfiffa wacce take ci a kowacce Talata.
Saurari Rahoton Souley Moumouni Barma
Your browser doesn’t support HTML5