Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Bukaci Kungiyar Kasashen Nahiyarta Ta Dakatar Da Kasar Venezuela


Mike Pompeo, sakataren harkokin wajen Akurka a taron OAS
Mike Pompeo, sakataren harkokin wajen Akurka a taron OAS

Sakataren Harkokin Wajen Amurka Mike Pompeo ya kira kungiyar kasashen nahiyar Amurka ta dakatar da kasar Venezuela daga kungiyar saboda zargin cewa ta gudanar da zaben bogi a kasarta

Sakataren harkokin wajen Amurka, Mike Pompeo, ya yi kira ga kungiyar kasashen nahiyar Amurka ko kuma OAS a takaice, da ta dakatar da Venezuela daga kungiyar, har sai ta daidaita abin da Amurka ta kwatanta a matsayin “zaben bogi” da aka yi, wanda ya bai wa shugaba Nicolas Maduro sabon wa’adin mulki a watan da ya gabata.

Pompeo ya zargi gwamnatin Maduro da “rusa turakun dimokradiya” inda ya fadawa taron kungiyar ta OAS mai kasashe 34 cewa, “abin takaici ne idan aka yi la’akkari da cewa al’umar Venezuela sun fuskanci matsalar fadawa cikin matsalolin rayuwa.”

Wannan kira na Pompeo, ya jaddada kiran da mataimakin shugaban Amurka, Mike Pence ya yi a watan da ya gabata, na cewa a dakatar da Caracas daga kungiyar.

To sai dai martanin da kungiyar ta OAS ta mayarwa Amurkan, bai fito karara ya fayyace matsayarta, inda ta ce, idan har za a dakatar da kasar ta Venezuela, dole sai kungiyar ta yi zama na musamman - a gefen taron da ta saba yi, kafin a tattauna batun.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG