Harin jirgin sama ya hallaka 'yan kungiyar al-Shabab su 7

  • Ibrahim Garba

'Yan Somalia na ta gudu daga wuraren tashe-tashen hankula

Shaidu sun ce wani harin jirgin sama ya hallaka wasu ‘yan kungiyar

Shaidu sun ce wani harin jirgin sama ya hallaka wasu ‘yan kungiyar al-Shabab mai alaka da al-Qaida su 7 a Kudancin Somaliya.

Harin jirgin saman ya auku ne da safiyar yau Jumma’a a wata tungar ‘yan tawayen da ake kira “Kilomita 60” da ke Kudancin Mogadishu, babban birnin kasar.

Hukumomin sun ce wani kwamandan al-Shabab na cikin wadanda aka kashe lokacin da wani makami mai linzami daga wani jirgin da ba a bayyana ba ya dira kan wata mota. Wani wakilin Sashen Somalia anci na Muryar Amurka y ace wadanda su ka mutu din sun hada da ‘yan kasashen waje 4 da ‘yan Somaliya 3.

Babu wanda ya dau alhakin kai harin. An san dakarun Amurka da kai hare-hare a Somaliya, kamar kwanan nan da dakarun kundunbalan na ruwa su ka ceto wasu ma'aikatan agaji su biyu da mafasan ruwa ke rike da su.

A wani al'amari kuma na dabam, al-Shabab ta fito da wani faifan bidiyo na abin da ta kira wani sojan Kenya da ta kama. A bidiyon, sojan, wanda aka bayyana shi da cewa Edward Mule Yesse ne dan shekaru 30 da haihuwa ya yi kira ga gwamnatin Kenya da ta janye dakarunta daga Kudancin Kenya, inda su ke fafatawa da al-Shabab tun daga watan Oktoba.