Ma'aikatar lafiya a yankin da ke karkashin mamaye a Yammacin Gabar Kogin Jordan ta ce an kashe mutum guda kuma mutane tara sun jikkata a wani samame da Isra'ilar ta kai kan wani sansanin 'yan gudun hijira, yayin da sojojin Isra'ila suka ce a ranar Asabar sun bude wa wasu "yan ta'adda" wuta.
Wani matashi mai shekaru 18, Muhammad Medhat Amin Amer, "ya mutu sakamakon harbin bindiga a sansanin Balata" da ke arewacin yankin, a cewar ma’aikatar lafiya ta Palasdinawa ta fada a daren Juma’a, tana mai cewa mutane tara sun jikkata, "hudu daga cikinsu suna cikin mawuyacin hali."
Kungiyar ba da agaji ta Red Crescent ta Palasdinawa ta ce samamen ya fara ne da daren Juma’a kuma ya haifar da arangama mai tsanani.
Kamfanin Dillancin labarai na Palasdinawa, Wafa, ya ruwaito cewa sojojin Isra'ila sun shiga sansanin ta shingen bincike da ke Awarta inda suka saka gwanayen harbi a kan rufin gine-ginen da ke kewaye."
A wata sanarwa da aka fitar a ranar Asabar, sojojin Isra’ila sun ce yayin aikin "yaki da ta’addanci," "yan ta’adda sun sanya abubuwan fashewa a yankin domin cutar da sojojinsu, sun kuma jefa abubuwan fashewa, sannan sun cilla wuta a kan dakarun."