Harin Bam A Mugadishu Ya halaka Mutane Akalla 70

Sojojin gwamnatin Somalia suke dauke da gawar wani da harin kunar bakin wake ya kashe.

Hukumomin kasa da kasa suna bayyana bakin cikinsu kan harin bam da aka nasa cikin babbar motar dakon kaya data raba wani ginin gwamnati gida biyu a Mugadishu babban birnin Somalia, ya halaka mutane akalla 70, da jikkata wasu da dama.

Hukumomin kasa da kasa suna bayyana bakin cikinsu kan harin bam da aka nasa cikin babbar motar dakon kaya, data raba wani ginin gwamnati gida biyu a Mugadishu babban birnin Somalia, ya halaka mutane akalla 70, da jikkata wasu da dama.

Babban sakatern majalisar dinkin Duniya Ban ki-moon ya fada jiya talata yace yana cike da takaicin abin da ya kira “mummunar hari”. Yace abu ne mai wuya a gane dalilin da za’a auna hari kan farar hula da basu aikata ko wani irin laifi ba.”. Ya kara d a cewa babban baun bakin cikin shine harin yazo a dai dai lokacin da shugabannin siyasar kasar baki daya suke aiki domin cimma zamna laifya.

Kungiyar mayakan saki al-shabab ta dauki alhakin kai harin, tana mai cewa ta auna shi kan gwamnatin wucin gadin kasar da sojojin kiyaye zaman lafiya na tarayyar Afirka domin taimakawa gwamnatin wucin gadin kasar.

Kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya yayi Allah wadai d a harin, ta sake jaddada goyon bayanta ga gwamnatin wucin gadin kasar, tana mai cewa duk wani nau’in ta’addanci laifi ne d a bashi d a madogara”.

Amurka tayi Allah wadai da abinda ta kira rashin mutunta raid a al-shabab take nunawa, Ingila ta kira harin ragwanci,Faransa kuma ta kira harin da cewa mugunta ce muraran”.

Galibin wadanda harin ya rutsa dasu dalibai ne da suka zo ma’aikatar ilmi da suka zo duba sakamakon jarrabawa domin samun gurbin karon ilmi a Turkiyya.

Ahalin yanzu kuma Majalisar Dinkin Duniya tace fada da ake gwabzawa a kudancin kasar, ya tilastawa kungiyoyin aikin agaji dakatar ayyukansu a gari dake da muhimmanci a yaki d a yunwa da ta addabi kasar.