Hari Kan Layin Lantarki Ya Jefa Abuja Cikin Duhu

Ma'aikata na gyara a wasu turakun wutar lantarki a Najeriya (Hoto: X/TCN)

An riga an tura tawagar injiniyoyin TCN zuwa wurin, kuma suna aiki tukuru domin sake mayar da wayar da aka lalata daga iya daukar lantarki mai karfin 330kv.

Wasu sassa na birnin tarayyar Najeriya, Abuja, sun afka cikin duhu bayan da barayi suka sake lalata babban layin lantarki na Shiroro zuwa Katampe mai karfin kilovolt 330.

Sanarwar da mai magana da yawun kamfanin samar da lantarki na Najeriya (TCN), Ndidi Mbah, ya fitar a daren jiya Alhamis, tace da misalin karfe 11 da mintuna 43 na dare, layin lantarkin daya hada Shiroro da Katampe mai karfin 330 ya yanke daga kan babban layin kasa.

“TCN na takaicin sanar da cewar an lalata layin lantarkinsa daya tsahi daga shiror zuwa katampe mai karfin 330kv a ranar laraba, 18 ga watan disamban 2024.

Mbah ya kara da cewa an riga an tura tawagar injiniyoyin TCN zuwa wurin, kuma suna aiki tukuru domin sake mayar da wayar da aka lalata daga iya daukar lantarki mai karfin 330kv.

“Ana sa ran dawo da lantarki kan layin nan bada jimawa ba,” a cewarsa, inda ta bukaci al’umma dasu taimaka wajen ganowa tare da bada rahoton duk wani motsi da basu yarda da shi a kewayen turakun lantarkin.