Jerin hare-hare kan akwatunan zabe a sassan Amurka na kara kaimin matsin lambar da jami’an jiha da na kananan hukumomi ke fuskanta, wadanda ke fatar sa ido domin ganin an gudanar da zaben shugaban kasar da ke tafe lami lafiya.
Hakan na faruwa ne yayin da masu kada kuri’unsu da wuri a suka zuwa yin zabe ayawan sassan kasar da kuma yayin da miliyoyin Amurkawa za su fita rumfunan zaben a mako mai zuwa idan Allah ya kaimu.
Jihar Washington da ke arewa maso yamma na Amurka, ta tabbatarwa da Muryar Amurka cewa a ranar Litinin din nan ‘yan sanda a jihar da hukumar binciken laifuffuka ta FBI na gudanar da bincike kan rahotannin da aka samu na wata na’ura da aka dana a akwatunan tattara kuri’u a Vancouver, ta Washington a ranar ta Litinin.
Jami’ai sun ce, babu wanda ya jikkata, amma dai wasu daga cikin akwatunan tattara kuri’un sun lalace.
Faifan bidiyon da jami’an yankin suka samar ya nuna yadda ‘yan kwana-kwana suka rika kokawar kashe wuta a wurin, aka kuma ga yadda akwatunan kuri’ar suka rika cin wuta a kasa.