Attajirin ba'amurken nan mai ba da tallafi, Bill Gates, ya bayyana cewa harajin da ake tarawa a Najeriya ya yi karanci ainun.
Attajirin, wanda ya kasance daya daga cikin shugabannin gidauniyar “Bill and Melinda Gates” ya bayyana hakan ne a dandalin “nutrivision” na bana; inda matasa ke tattaunawa a kan hanyoyin samar da abinci mai gina jiki a nahiyar Afirka da ya gudana a Abuja, babban birnin Najeriya.
Bill Gates na martani ne a kan tambayar da aka yi masa game da dabarun da gwamnatin tarayyar Najeriya ka iya dauka wajen ba da tallafin makudan kudade a harkar kiwon lafiyar al’umma.
“Tsawon shekaru, akwai tsare-tsaren da Najeriya ke da su na daukar dawainiyar gwamnati fiye da yadda al’amarin yake a yanzu. Amma ainihin harkar tattara haraji a Najeriya ta yi karanci matuka.”
Ya kuma kara da cewa Najeriya na iya zama kasa mai fitar da kayan abinci zuwa ketare duba da girma da albarkar kasar.
Bill Gates ya cigaba da cewa, ‘yan Najeriyar da ke bukatar ilimi da lafiya na iya dogaro a kan wasu tsare-tsaren gwamnati da na daidaikun jama’a.