'Yan takaran shugaban kasa irin su Donald Trump da ake cewa basu cancanci suyi nasarar cin zabe ba kamar yadda wasu ke cewa, to sai dai kuma an samu akasi a cikin ‘yan watanni da suka gabata ga bisa dukkan alamu wanan dan taklikin shine zai lashe wannan zaben fidda gwani.
Hamshakin mai kudin nan Trump wanda bai taba rike ko wane irin mukamin gwamnati ba,yayi nasara akan abokan takarar sa na jamiyyarsu ta Republican, domin ko ya lashe zaben ranar Talata wanda yake shine yafi ko wane zabe tasiri a zaben fidda gwani na takarar shugabancin Amurka.
Yayin da yake kan hanyar lashe zaben fidda gwani, Trump yayi suna ne wajen tado da maganganu masu jan hankali dake kawo rudani da cece kuce cikin kasa dama duniya baki daya, musammam akan abinda ya shafi tsaro, harkokin shige da fice kuma sau tari yana danganta wadannan batutuwa da abokan karawar sa.
Sai dai wasu na cewa wannan matakin ko tsarin da Trump ya bi shine wata sabuwar dabarar janyo hankalin masu zaben fidda gwani a cikin manyan jamiyyun biyu na Amurka.
Kana da zaran dan takara ya samu zaben rike tutar jamiyyar su to mataki nagaba kuma shine sai ya daidaita kalaman sa domin ganin ya janyo hakali Amurkawa wajen zaben gama gari.