Har Yanzu Kananan Yara Da Dama Suna Mutuwa A Najeriya

Wayansu yara a wani shirin UNICEF

Asusun UNICEF yace, Najeriya bata sami cin gaba ba sosai a fannin shawo man mace macen kananan yara.
Asusun tallafawa kananan yara – UNICEF ya bayyana cewa, har yanzu Najeriya bata sami cin gaba ba sosai saboda har yanzu kananan yaran da suke mutuwa da shekarunsu basu kai biyar ba yana ci gaba da karuwa.

Ms. Jean Gough wakiliyar asusun a Najeriya ce ta bayyana haka a Abeakuta, jihar Ogun. Ta ce duka da yake sauran kasa da kwanaki dubu a kai lokacin da kasashen duniya suka dibarwa kansu na shawo kan wadansu muhimman matsaloli, har yanzu Najeriya ba ta sami ci gaba a kokari a fannin shawo kan matsalar mace macen kananan yara da shekarunsu basu kai biyar ba.

Bisa ga cewar Gough, kashi ashirin bisa dari na mace macen kananan yara da ake yi a nahiyar Afrika yankin Hamada suna faruwa ne a Najeriya. Tace wannan ya sa hankalin kasashen duniya suka koma idan aka tashi tattaunawa a kan batun mutuwar kananan yara.

A farkon wannan karnin, kasashen duniya suka amince da cewa zasu rage yawan mace macen kananan yara da kashi biyu bisa dari kafin shekara ta dubu biyu da goma sha biyar.

Tsakanin shekara ta dubu biyu da dubu biyu da goma sha daya, yawan kananan yaran dake mutuwa kafin shekarunsu ya kai biyu ya ragu da kimanin kashi arba’in da biyar bisa dari a duk fadin duniya, sai dai wannan bai nuna cewa haka yake a duk kasashen duniya ba a kasashe kamar Najeriya da Indiya da Congo da Pakistan da kuma China.

Tace duk da ci gaban da kokarin da ake yi, ana kara samun karuwar mace macen kananan yara a Najeriya a maimakon raguwa. Wani rahoto da aka fitar kan ci gaban da aka samu ya nuna cewa, yawan kananan yaran dake mutuwa kafin su cika shekaru biyar a duniya ya karu a Najeriya daga kananan yara dari da talatin da takwas a cikin kowanne kanannan yara dubu daya a shekara ta dubu biyu da bakwai zuwa dari da hamsin da takwas a cikin dubu biyu da goma sha daya.

Wannan na nufin cewa, yara dari da hamsin da takwas daga cikin yara dubu zasu mutu kafin su cika shekaru biyar. Abin takaici shine, ana iya maganin yawancin dalilan mace macen, kamar tsabta, da abinci mai gina jiki da kuma sauya halayen dake da illa ga ceton rayukan kananan yara.