A matsayin matakin farko na cimma wannan burin, cibiyar tace za a samar da magunguna ga dukan mutanen da suke bukata dake dauke da kwayar cutar HIV.
Bisa ga rahoton, za a yi amfani da wani sabon tsarin jinya da Hukumar Lafiya ta duniya ta tsara wajen yiwa a kalla kashi tamanin bisa dari na masu fama da cutar ko kuma wadanda ke fuskantar hatsarin kamuwa da ita jinya da samar masu da rigakafi.
Cibiyar tace tsarin jinyar da aka ba lakabi da suna “jinyar 2015” zai samar da dabaru da kuma hanyoyin kara yawan cibiyoyin jinya yadda masu bukata zasu iya samun magunguna da taimakon da suke bukata cikin sauki, abinda zai taimake su su kasance cikin koshin lafiya ya kuma hana wadansu daukar cutar.
Rahoton ya nuna cewa, daukar wannan matakin zai taimaka wajen inganta lafiyar matasa da kuma wadanda suke da karfin aiki. Bisa ga rahoton, zuba jari wajen jinyar cutar HIV zai taimaka wajen bunkasa tatalin arziki har sau uku, ya kuma hana kananan yara zama marayu, da kuma amfani da kudin da za a kashe wajen jinyar cutar a kan biyan bukatar iyali.
Shirin yaki da cutar HIV mai lakabi “Jinyar 2015” (Treatment 2015) ya bada karfi wajen gwajin kwayar cutar HIV da jinya a maimakon neman mutane su saba da bin matakai masu wahala na jinya.