Har yanzu hukumomin jihar Yobe na kokarin tattara adadin 'yan matan dake karatu a makarantar sakandare dake garin Dapchi da 'yan kungiyar Boko Haram suka kai ma hari yammacin Litinin din da ta gabata.
Tun daga ranar iyaye da abokan arzki suka dinga ziyartar makarantar domin cigiyar 'ya'yansu da wadanda suka sani. Wasu da suka gano 'ya'yansu su na sambarka wasu kuma da har yanzu babu labarin nasu sun mika wa Allah lamarin.
Wannan lamarin yayi kama da harin da aka kai, har aka sace daliban makarantar mata dake Chibok a jihar Borno da aka yi a shekarar 2014.
Alhaji Muhammed Amin kwamishinan ilimi na jihar Yoben a cewarsa ana samun wasu yaran a kauyukan da suka gudu. Amma yanzu ba zasu iya tabbatar da adadin yaran da aka sace ba. Sai dai yanzu gwamnatin jihar ta rufe makarantar.
Wani mahaifin da har yanzu bai san makomar 'yarsa ba ya ce an samu labarin wasu amma tasa babu duriyarta sam. Ya dukufa da rokon Allah Ya dawo da ita gida lafiya.
Ga rahoton Haruna Dauda da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5