Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Saki Mutane 475 Da Aka Tuhuma Da Cewa 'Yan Boko Haram Ne A Najeriya


Hukumomin najeriya sun saki karin mutane 475 wadanda aka tuhuma da kasancewa 'yan Boko Haram, a saboda babu wata shaidar da ta nuna hakan a lokacin da aka fara shari'arsu.

Ma'aikatar shari'a ta Najeriya, ita ce ta bayyana wannan jiya lahadi, a bayan da aka shafe mako guda ana ci gaba da shari'ar wadannan mutane da ake tuhuma a gaban wata kotun dake cikin wani sansanin sojojin Najeriya a Jihar Neja.

Kakakin ma'aikatar, Salihu Othman Isah, yace a ranar jumma'a aka bayar da umurnin sakin mutanen, inda yace su wadannan mutane 475, za a mika su ga gwamnatocin jihohinsu wadanda zasu dauki matakan sake tsugunar da su kafin a kyale su su koma cikin jama'a.

Yace an kama wadannan mutane ne bisa zargin ko dai su na cikin kungiyar Boko Haram, ko kuma sun boye bayanan inda 'yan kungiyar suke, ko kuma irin ayyukan da suke kullawa.

Yace masu gabatar da kara sun kasa tuhumarsu da aikata wani abu a saboda babu wata shaidar da ake da ita a kansu. Don haka ne aka bayar da umurnin a sake su.

Daga cikin wadanda aka sake har da wata karamar yarinya tare da jaririyarta daga jihar Borno, wadda wani yayanta ya dauke ta ya kai ta cikin wani sansanin 'yan Boko Haram ya kuma aurar da ita ga wani abokinsa tun tana da shekaru 11 da haihuwa. An kama ta a shekarar 2014 a lokacin da take kokarin tserewa.

Haka kuma an saki wasu tagwaye makanikai su biyu da aka kama a Jihar bauchi a shekarar 2010, bayan da suka gyara wata motar dan Boko Haram.

Ya zuwa yanzu dai, an yi shari'ar mutane kusan dubu 1 da 700 a shari'ar da aka fara cikin watan Oktoba a wannan kotu ta musamman dake cikin sansanin sojan.

Wasu daga cikin mutanen sun shafe shekaru masu yawan gaske ba a yi musu shari'a ba.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG