Gwamnan jahar Kaduna malam Uba Sani wanda ya sanar da sako daliban da kan shi ya dauki lokaci yana ganawa da jami'an tsaro da kuma iyayen daliban sai dai bayan wani dogon lokaci sai aka umarci iyayen daliban su koma gida su dawo litinin, 03/25/2024.
Tun da sanyin safiyar jiya Lahadi dai manema labaru su ka yi dafifi a gidan gwamnatin jahar Kaduna don gane wa idanunsu daliban da aka ce an sako sai dai bayan kwashe sa'o'i daga bisani sai aka sallami iyayen daliban tare da alkawarin cewa yau litinin su dawo don karbar daliban.
Wasu daga cikin iyayen daliban da su ka yi magana da manema labaru dai sun ce ba za su zake wajen bayani ba saboda su kan su ba su san ko dalibai nawa aka sako ba.
Salon sanar da sako daliban garin Kurigan da gwamnatin jahar Kaduna ta yi da kuma jinkirin bayyanar daliban dai sun jawo tantama da tura tambayoyi tsakanin masana harkokin tsaro irin su manjo Yahaya Shinko mai-ritaya wanda ya ce akwai wasu batutuwan dubawa.
Yanzu tambayar da wasu ke yi ita ce shin kubutar da daliban aka yi ko kuwa sako su aka yi masamman ganin tun ranar da aka sace daliban dama gwamna Uba Sanin jahar Kadunan ya lashi takobin kubutar da su koma ya ya zai yi.
Neman sanin adadin daliban da aka sako, lafiyar su, hanyar da aka bi wajen sako su, maganar kudin fansa ko saka karfin soja, na cikin wasu daga cikin tambayoyin da ake sa ran samun amsoshin su yau Litinin idan gwamnati ta gabatar da wadannan dalibai gaban manema labaru.
Saurari rahoton Isah Ikara:
Your browser doesn’t support HTML5