A ranar 29, ga wannan watan ne gwamnatin shugaba Muhammad Buhari zai cika shekaru biyu akan mulki.Sai dai har yanzu ‘yan kasar na korafi game da yadda gwamnati ta raba ma’aikatun kasar musamman ta wutar lantarki wanda ke zama kashin bayan ci gaba.
Har yanzu ana ci gaba da fuskantar matsalar karanci wutar lantarki a kasar wanda ake ganin cewa aikin ya yiwa Minista Babatunde Raji Fashola, yawa.
Daya daga cikin ma’aikatar da har yanzu ‘yan Najeriya, ke korafi akai itace ma’aikatar da aka ware wa tsohon gwamnan jihar Lagos, Babatunde Raji Fashola, watau na kula da ma’aikatar samar da wutar lantarki hanyoyi da kuma gidaje har yanzu dai jama’a na ci gab da kukan cewa basu gani a kasa ba masamman bangaren wautar lantarki wanda matsalarsa yaki ci yaki cinyewa.
Wasu ‘yan Najeriya, da wakilin muryar Amurka Babangida Jibrin, ya zanta dasu sun bukaci gwamnatin ta sake sa ido akan batun ma’aikatar wutar lantarki, hanyoyi da gidaje da zammar raba ma’aikatar ko aiki zai wa Ministan sauki.
Fatar ‘yan Najeriya shine na ganin cewa an samu daidaito na wutar lantarki domin samar da ci gaban kasa kamar yadda gwamnati keda burin ganin an samu kafin nan da dan wani lokaci.
Your browser doesn’t support HTML5