Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sabon Shugaban Koriya Ta Kudu Zai Tura Tawaga China


Sabon Shugaban Kasar Koriya Ta Kudu Moon Jae-In
Sabon Shugaban Kasar Koriya Ta Kudu Moon Jae-In

Shugabannin akasashen biyu sun yi magana ta wayar tarho kwana daya kafin a rantsar da Moon Jae-In don maye gurbin tsohuwar shugaba Park Geun-Hye da aka tsige daga mukaminta.

Ofishin sabon shugaban kasar Koriya ta kudu Moon Jae-In ya fada yau Alhamis cewa shugaban na shirin tura wata tawagar wakilansa China don tattaunawa akan shirin Nukiliyar Koriya Ta Arewa da kuma damuwar China akan makami mai linzami na kariya da Amurka ta girke a Koriya Ta Kudu.

Wani mai magana da yawun shugaba Moon yace shugabannin sun amince akan bukatar kawar da duk wasu makaman nukiliya a yankin Koriyoyin biyu, kuma Moon ya gamsu da damuwar China akan makamin kariyar THAAD da Amurka ta girke.

China dai na ganin wannan makamin na THAAD a matsayin wata barazana ga ita kanta, wanda kuma zai iya bata zaman lafiyar yankin da ake ta yiwa cin kwan makauniya. Sannan tuni ta mayar da martani ta hanyar takaita shiga da kayayyaki daga Koriya ta Kudu da ma masu yawon bude ido.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG