MDD ta bada rahoton cewa ana cigaba da samun Karin ‘yan Iraki masu gudun hijira sakamakon farmakin da sojoji ke kaiwa don sake kwato birnin Mosul dake Arewacin kasar daga hannun ‘yan ISIS.
WASHINGTON, DC —
Fadan dai ya kai fiye da wata daya ana yin sa da dakarun Iraki, da mayakan kurdawa da na ‘yan shi’a a dannawar da suke yi daga wajen garin zuwa cikinsa. Mayakan ISIS sun kame garin Mosul, gari mafi girma na biyu a Iraki, kusan fiye da shekaru 2 da suka gabata.
A wani rahotonta na baya-bayannan, ofishin bada agajin MDD ya fadi cewa mutane dubu sittin da shida da dari biyar da hamsin sun rasa matsugunnansu, mutane 14,000 daga cikinsu a makon da ya gabata su ka yi gudun hijira. Ta kuma yi gargadin cewa yayinda fadan ke kai ga wuraren dake da runtsi a birnin na Mosul, ta yiwu a sami karin mutanen dake tserewa daga birnin.
Kungiyar bada agajin Iraki da ake kira Red Crescent ta ce adadin masu gudun hijirar yanzu ya kai fiye da 85,000.