Jaimyyar PDP ta zargi jamiyyar APC da nufin tashin hankali wanda zai wanda zai kawo tsaiko a zaben gwamnoni da yan majilisar dokoki a jihar ta Ribas Jamiyyar APC tace tana zargin jamiyyar PDP da shigowa da makamai a cikin jihar da nufi anfani dasu domin tada hankulla da kuma razana masu zabe, jamiyyar PDP ita kuma ta kafe akan cewa jamiyyar PDP ce ke kawo tashin hankali
‘’Mr Philip Abuwa shugaban jamiyar PDP a jihar ta Ribas yana cewa mukan banu ruwan mu, jamiyyar APC ce ke rura wutan rikici a wannan jihar tamu ta Ribas, ita kuwa jamiyyar APC a jihar ta Ribas tace hare-haren da ake kaiwa sun yawaita inji dan takarar gwamna a tutar jamiyyar APC Dr Dakuku Adol Peterside ke fadi.
‘’Shedu da dama sunga dan majilisar dokoki ya bada umurnin a bude wuta kan magoya bayan jamiyyar APC, duk kuwa da wannan rudani da aka shiga a jihar ta Ribas rundunar yansanda tace ta shirya wa zaben HassanKarma shine kwamishinan yan sandan da aka turo domin gudanar da zabe a jihar.
‘’Mun gaya wa yan Ribas cewa namu dai munzo mu yi musu aiki kowa da kowa ya samu damar yaje ya jefa kuriaar say a dawo gida kuma munyi musu gargdi cewa duk wanda yake neman masifa to ya bar wannan zance yanzu ana neman wanda zai shugabanci jihar ne ba fada ake so ba, wanda kuma yaki bin umurnin mu to za a kama shi, mu da sojoji da jamiaan tsaro masu sanye da farin kaya muna tare munyi taro kuma mun amince cewa daga tsakada daren ranar alhamis wato karfe 12 za a hana mutane zirga-ziga har sai karfe 5 na safiyar gobe, irin wurare kamar su water front muna da sojojin ruwa a wurin, munsa sojojin ruwa suyi sintiri haka kuma sojojin sama suma suna shawagi da jiragen su masu saukar ungulu kasa-kasa duka su duba duk abinda ake yi, duk wanda baida kuriaar da zaije ya jefa to kar ya fita, to kuma munji cewa akwai mutanen da suka je suka dinka kayan yan sanda dana sojoji duk wanda aka samu da wannan to za a kama shi’’
Zuwa yanzu an nuno rundunar sojan jihar Ribas sun kame wasu mutane su 3 da bindigogi samfurin AK 47 a jihar.