Ana yawan kuka da kafafen yada labaran gwamnatin tarayyar Najeriya bisa zargin take ‘yancin wani bangare da kuma yiwa wani bangare alfarma. A misali yadda wasu tashoshin kasar ba su ba wa ‘yan adawa damar yada manufa a kafafen yada labaran gwamnati ba.
Wani dan jarida daga jaridar Blueprint a Najeriya mai suna Mohammed Shitu yayi tsokacin cewa hakan bai kamata ba a matsayin ‘yan jarida. Yana ganin cewa ba a bawa ‘yan adawa dama tare da dankwafe su ne don kar su tona asirin yadda gwamnati mai ci ke mulkin jama’a da boye duk wasu kura kurai.
Ga wadanda suka san da cewa akwai hukumar gwamnatin tarayya mai kula da ayyukan kafafen yada labarai da kuma taka musu birki idan za su zarce makadi da rawa.
To amma abin mamakin shine yadda ba a ganin suna yin yadda ya kamata wajen ganin an bawa kowa damar da ta cancanta ya samu daga masu mulki har wadanda ba mulkin a hannunsu.ace hakan illa ne ga siyasa don zai kawo tsaiko wajen gane mulkin da ake tafiyarwa don jama’a. Daga karshen hirar tasa da Mahmud Lalo.
Su kansu hukumar ta NBC mai kula da kafafen 'yada labarai sun fada a kwanakin baya a hirar dayn su da Muryar Amurka cewa zasu dauki matakin cin tara gamae da wadannan saba dokar da aka samu a kafafen yada labaran gwamnati da masu zaman kansu.
Abin tambaya anan shine, shin me yasa sai yanzu shirin daukar matakin ya biyo baya bayan da jam'iyyar adawa ta lashe zaben shugaban kasa a zaben da ya kamata? Mohammed Shitu ya fada mana yadda hakan bai dace da 'yan jarida ba.