Hanyar Kyautata Musanyar Bayanai Don Kare Harin Ta'addanci

Amurka ta ce akwai karin abubuwan da suka zamo tilas a yi su wajen kyautata musanyar bayanan leken asiri a Turai, a bayan munanan hare-haren ta’addanci na makon jiya a birnin Brussels.

Kakakin fadar shugaban Amurka ta white House, Josh Earnest, yace hare-haren da aka kai kan filin jirgin sama da kuma tashar jiragen karkashin kasa a Brusels sun sake nuna muhimmancin yin aiki sosai da tsare-tsaren ayyukan leken asiri da tsaron kasa.

Ya sake jaddada goyon bayan Amurka ga Belgium a binciken da take gudanarwa.

Babban mai gabatar da kararraki na tarayya na Belgium ya fada jiya litinin cewa ala tilas hukumomi suka saki wani mutumin da aka yi ta yada rahotannin cewa yana daya daga cikin jigogin kai harin a saboda babu wata hujja ko shaida ta tsare shi. Kafin a sake shi, wannan mutumi da ake kira Faysal C ya fuskanci tuhumar shiga kungiyar ta’addanci, da kisan kai na ta’addanci da kuma yunkurin kisan kai na ta’addanci.