Hannayen Jari Sun Fadi A Kasuwannin Duniya Bayan Farfadowar Da Su Ka Yi

  • Ibrahim Garba

Wani dan hada-hadar hannayen jari kenan ke karanta farashinsu.

Kusan hankula sun kwanta yau Laraba a birnin London to amman zanga-zangar da ta addabi

Kusan hankula sun kwanta yau Laraba a birnin London to amman zanga-zangar da ta addabi babban birnin na Burtaniya cikin yan kwanakin nan ta bazu zuwa wasu birane, ciki hard a Manchester da Birmingham.

‘Yan sandan Birmingham sun ce mutane uku sun mutu bayan da wata mota ta kade su lokacin zanga-zangar. Mutane ukun na kokari ne su kare al’ummarsu daga masu wasoson dukiyar jama’a. ‘Yan sanda sun damke wani mutum kuma za a yi bincike game da kisan kan.

Shaidu sun ce daruruwan matasa sun yi ta farfasa tagogi da wasoson shaguna da kuma kokkona gine-gine a Manchester, birni na uku a girma a Burtaniya. ‘Yan sanda dai sun damke mutane 47 kan zanga-zanga ta baya-bayan nan.

Tarzoma ta barke ne dai a satin day a gabata bayan da ‘yan sanda su ka harbe wani magidanci dan shekara 29 mai ‘yaya 4 har lahira a wata unguwar talakawa mai suna Tottenham. Wasu rahotanni sun ce mutumin ya harbi ‘yan sanda da wata ‘yar bindiga ne bayan das u ka tsaida motar tasi dinsa. To amman wani rahoton ‘yan sanda na ran Talata y ace ba a harha ‘yar bindigar da aka samu a wurin ba. Har yanzu dai ba a san dalilin harbin mutumin da ‘yan sanda su ka yi ba.