Hankulan 'Yan Rajin Kare Dimokradiya A Nijer Ya Karkata Wajen Taron Amurka Da Afirka

Babban taron Amurka da shugabannin kasashen Afirka

Masu rajin kare dimokradiya a jamhuriyar Nijer sun yi na’am da taron da ake shirin farawa a yau Talata 13 ga watan disamba a nan birnin Washington DC a tsakanin kasar Amurka da kasashen nahiyar Afirka.

Wannan shine karo na 2 da shugaba Joe Biden ke shirya irin wannan taro da nufin tattaunawa akan hanyoyin kara inganta huldar dake tsakanin Amurka da kasashen Afirka wadanda aka yi amanna hukumominsu na kwatanta gudanar da mulkin dimokradiya.

Kasashen 49 daga cikin 55 na nahiyar Afirka ne aka sanar cewa sun sami takardar gayyata domin halartar wannan babban taro da zai gudana a karkashin jagorancin shugaba Joe Biden na Amurka.

Tun a yammacin Lahadin da ta gabata ne tawagar Nijer a karkashin jagorancin Shugaba Mohamed Bazoum ta tashi daga birnin Yamai don zuwa kasar ta Amurka domin halartar wannan zama da zai maida hankali akan fannonin da suka hada da Dimokaradiya, shugabanci da sha’anin tsaro.

Da yake bayyana ra’ayinsa Shugaban kungiyar FCR, Souley Oumarou ya yaba da wannan yunkuri na gwamnatin Amurka wanda a cewarsa babu tantama abu ne da zai amfani Afirka fiye da yadda abin yake a tsakaninta da sauran manyan kasashen duniya.

Masanin doka, bugu da kari shugaban gamayyar kungiyoyin Reseau Esperance, Bachar Maman wanda ke kallon wannan taro da mahimmanci ya shawarci gwamnatin Amurka ta kara duba halin da al’umomin Afirka ke ciki a yau sanadiyar halin da aka shiga a duniya.

Koda yake akwai alamar ci gaban dimokrdaiya a wasu kasashen nahiyar, ‘yan fafutika na fatan ganin Amurka ta yi amfani da wannan haduwa don ja hankulan shugabanni akan dimokradiya ta gaskiya.

Halin da ‘yan Diasporar Afirka ke ciki a Amurka da batun shugabanin matasan Afirka, kiwon lafiya, sha’anin cimaka da makamashi da hanyoyin zurga zurga na daga cikin batutuwan da kasashen Afirka da kawarsu Amurka zasu tabo a wannan babban taro wanda a karkashinsa gwamnatin Biden ke fatan kara inganta matsayin da ke kansa a gogayyar da ke tsakanin manyan kasashen duniya don karfafa huldarsu da nahiyar ta Afirka.

Saurari rahoton a sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

MATSAYIN YAN FAFUTIKA AKAN TARON US DA AFRIKA.mp3