ABUJA, NIGERIA - Rahotanni na nuna cewa masu neman mukaman minista da manyan masu ba da shawara na kamun kafa don samun gurbi a gwamnatin shugaba Tinubu.
Mukarrabin shugaba Tinubu, wanda ya yi rikon mataimakin dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC a zaben 2023 Ibrahim Kabir Masari, ya ce ya na da kwarin gwiwa za a yi sabon zubi a wajen mukaman.
Masari ya ce duk da cewa wasu da dama a tsohuwar gwamnatin Buhari na bin kafa don sake dawowa kan kujera, hakan na da wuya ainun.
"Duk wanda ya rike mukami a tsohuwar gwamnatin Buhari ya dace ya koma gefe ya rungumi wata sana'ar don ba wa wasu damar gwada tasu basirar," a cewar Masari.
Lauya mai zaman kan sa a Abuja Auwal Aldulkadir Albarudi, ya shawarci shugaba Tinubu da ya raba gwamnatinsa da jami'an gwamnatin Buhari, don hakan ne zai ba shi damar nada nasa mutanen don samun sauyi daga wadanda a ke zargi da almundahana.
In za a tuna tsohon shugaba Muhammadu Buhari bai yi alwashin tsaya wa mutanen sa ba, abinda kai tsaye ke nufin kowa ya debo da zafi bakin sa.
"Duk wanda ya neme ni na ba da wata shaida a kan sa a kotu to ko waye ya kuka da kan sa," inji Buhari.
Tsohon shugaban dai na London da wasu mafi kusaci a mukarrabansa, wadanda in ka gan su a wuri to ba mamaki tsohon shugaban na kusa.
Saurari cikakken rahoto daga Nasiru Adamu El-hikaya:
Your browser doesn’t support HTML5