Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ba Za Mu Zama ‘Yan Amshin Shata Ba – Abbas

Sabon Kakakin Majalisar Wakilan Najeriya, Tajudeen Abbas
Sabon Kakakin Majalisar Wakilan Najeriya, Tajudeen Abbas

A cewar Abbas, za su dukufa wajen samar da tsare-tsare da za su ciyar da kasa gaba tare da hadin kan bangaren zartarwa.

Sabon Kakakin Majalisar Wakilan Najeriya Tajudeen Abbas, ya ce, ba za su zama ‘yan amshin shata ba yayin wa’adin mulkinsu.

Ya bayyana hakan ne ga manema labarai a Abuja bayan wata ganawa da ya yi da Shugaba Bola Ahmed Tinubu a ofishinsa.

An zabi Abbas a matsayin shugaban majalisar ta wakilai bayan da ya samu gagarumar nasara a ranar Talata.

A lokuta da dama, akan zargi ‘yan majalisar dokoki da zama ‘yan amshin shatar bangaren zartarwa, zargin da sukan musanta.

A cewar Abbas, za su dukufa wajen samar da tsare-tsare da za su ciyar da kasa gaba tare da hadin kan bangaren zartarwa.

Wannan majalisa da aka kaddamar ita ce ta goma.

XS
SM
MD
LG