Da yake magana da manema labarai a filin Jirgin sama na Istanbul a yau Juma’a bayan yanke hukuncin akan Mehmet Hakan Atilla, mataimakin babban daraktan bankin bada rance mallakin Turkiyya Halk Bank.
Shugaba Tayyep Erdogan yace ala’amarin wani bangare ne mai tsaho daga shirye shiryen makirci akan kasarsa, inda Erdogan din yayi gargadi akan dokokin kasa da kasa tsakaninsu da Amurka sun rasa madafa.
Ya kara da cewa, “idan dai har wannan itace fahimtar shari’a a wurin Amurka to hakika duniya na cikin hadari, babu wata fahimtar shari’a mai kama da wannan”.
A baya mai magana da yawun jam’iyyar AKP dake mulki Mahir Unal, kai tsaye ya zargi Amurka. Inda ya rubuta a twitter cewa, “Dalilin wannan shari’a a Amurka, yin katsalanda ne a harkokin cikin gidan Turkiya".
Shugaban Turkiyyar ya ci gaba da cewa, wannan shari’ar da aka yi keta dokar kasa da kasa ne mai cike da hatsari da barazana ga harkar shari'a. A bayyane yake a wannan hukunci bamu da wani abin fada akai don muna tababarsa.