A duk inda jama'a suka botsare a bisa son canji ko kosawa da wasu matakan gwamnatin kasashensu, wasu kasashen suna amfani da karfin tuwo wajen takura masu zanga- zanga don murkushe su. Kamar yadda hakan ta faru a su Libya da makamantansu amma sai kwalliya bata biya kudin sabulu ba.
Amfani da karfin tsiya da gwamnatocin kasashen Larabawa suka yi wajen neman murkushe zanga-zangar data yi farin jini a shekara ta 2011 su suka kai ga hambare gwamnatoci a Masar da Libya, da kuma haddasa yakin basasa a Syria.
Iran ta fuskanci kwatankwacin zanga-zangar da aka yi a kasashen Larabawa a shekara ta 2011 a cikin 'yan kwanakin nan, amma sai ta tura 'yan sanda kalilan, matakin da ya sanya zanga-zangar ta lafa.
Wanda hakan ce ta sa masu nazarin al'amura ke ganin wata kila Farisar ta shafawa gemunta ruwa ne ganin yadda gemun kasashen Larabawa kamar Libya da Misira suka kama da wuta.
A yayin da suka yi amfani da karfi don murkushe zanga-zangar amma sai kilu ta jawo bau, har hakan ta yi sanadiyyar kifar da gwamnatocin nasu tare da hallaka ma wasu shugabanninsu.
Facebook Forum