An bukaci matasa da su jajirce wajen neman ilimi tare da tabbatar da an cimma burin da suka sa a gaba, a hannu guda kuma mutun ya dunga duban wadanda ya fi domin yiwa Allah godiya.
Wata matashiya Nafisa Ahmad Yaro, ce ta shedawa Baraka Bashir, haka a wata hira da suka yi.
Ta kara da jan hankalin matasa da su sa imani da yarda da kansu , tare da yin komai sabo da Allah , lallai zasu cimma burinsu na rayuwa.
Nafisa ta ce ta so ta karanci karatun lauya , sakamakon wani lalura bata sami damar kamala karatun nata ba a jami’a , inda ta dakata da karatu har na tsawon shekara biyu daga bisani ta canza layi inda ta karanci harkar siyasa.
Ta ce hakan bai sa tayi kasa a gwiwa ba, ta jajirce ta kamala inda ta sami takardar digirinta sannan ta fara koyarwa a wata makarantar firamare na karamar hukuma sannu a hankali har ta sami damar koyarwa a makarantar gwamnati.
Ta ce sakamakon jajircewarta da gwazon ta yasa ta sami gubin karatu a ma’aikatar gwamnatin tarayya.
Your browser doesn’t support HTML5