Farashin matakan kujerun uku sun hada da babbar kujerar tashi daga arewacin Najeriya wadda ta kama nera dubu dari takwas da tasa'in da bakwai da dari hudu da saba'in da shida da kwabo hamsin da tara.
Mai tashi daga kudu kuma zai biya nera dubu dari tara da biyar da dari biyar da hamsin da shida da kwabo hamsin da tara.
Matsakaiciyar kujera kuma daga arewa nera dubu dari bakwai da casa'in da takwas da dari hudu da saba'in da shida da kwabo hamsin da tara. Daga kudu kuma nera dubu dari bakwai da sittin da shida da dari biyar da hamsin da shida da kwabo hamsin da tara.
A zahiri an samu karin farashin kujerun daga wajajen nera dubu hamsin ga karamar kujera zuwa dubu dari ga babbar kujera.
Uba Mana babban jami'in hukumar alhazan ya bada misali. Yace bara nera bata wuce dari da hamsin ko da saba'in ba kan kowace dalar Amurka amma bana ta haura sama da nera dari biyu. To saidai gwamnatin tarayya ta ba mahajatta rangwame. Canjin dala yanzu ya koma nera dari da sittin. Idan bada ragwamen ba da farashin kowace kujera ya kai miliyan daya da wasu 'yan kai.
Abu na biyu da ya kawo hawa hawar farashi shi ne gyare-gyare da ake yi a Saudiya. Yawancin gidajen dake kusa da masallacin kaba an rushesu. Gidajen da ake zama da can yanzu babu su. An rushesu. Dole ne a nemi wasu amma kuma suna da tsada.
Kazalika gwamnatin tarayya ta amince da kamfanonin jirage takwas na cikin gida da ketare da zasu yi jigilar alhazan.Keftein Shehu Iyal tsohon jami'in gudanarwa na hukumar yace da suka fara aikin suna bin kamfanonin jirage da kudi suna roka a dauki alhazansu amma yau sai gashi Allah ya kawo wani yanayin inda kamfanonin ne da kansu suke rokon a bari su kwashi alhazan Najeriya.
Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5