Shugaban hukumar kwallon kafa ta Najeriya Amaju Pinnick ya bayyana cewa har yanzu kan hukumar a hade yake kamar yadda akan santa a matsayin tsintsiya madaurin ki daya duk da kwarya kwaryar ba hammata iskar da shugaban yayi tsakanin sa da Chris Giwa a yayin da suke gudanar da taron sasantawa a ranar larabar da ta gabata.
Taron wanda ministan matasa da wasanni Mr Solomon Dalong ya shirya ya tashi ne a yayin da rigima ta barke tsakanin mutanen biyu.
Koda shike wadanda aka shirya taron domin su wato shugaba hukumar kwallon kafar ta Najeriya da Mr Giwa domin sasanta ‘yar takaddamar da ke tsakanin su basu sami sasantawar ba kamar yadda ministan ya shirya, kuma Mr Amaju Pinnick ya ce ya godewa ministan domin kokarin da yayi na sasanta su.
Shugaba ya ce “muna so mu mika godiyar mu ga minister, da babban sakatare, da darakta janar a kokarin su na hada kan hukumar kwallon kafa ta Najeriya”.
Daga karshe Amaju Pinnick ya yi kira ga dukkan masu ruwa da tsaki a cikin harkokin kwallon kafar da su cigaba da mayar da hankali domin tabbatar da samun nasarori a dukkan wasannin dake gaban su.
Shugaban ya ce hukumar NFF na matukar farin ciki musamman ganin yadda kan hukumar ke hade har yanzu da kuma niyya da azamar da take domin samun nasarori.