A wani Sumamen badda kama da kungiyar hadin gwiwa da ya hada da shahararren mai farautar barayin nan Ali Kwara, tare da yan Sandan Najeriya sukayi, an cafke wani kwamandan yan maharba masu yakar Boko Haram da laifin sayar da makamai ba bisa ka’ida ba.
WASHINGTON, DC —
Kamar yadda bayanai ke cewa shi dai wanda aka kama mai suna Morris Enoch shine ya jagoranci maharban da suka taimakawa sojoji wajen yaki da yan Boko Haram a wasu kananan hukumomi dake Arewacin jihar Adamawa.
Morris Enoch, dai ya amsa wannan laifi da aka kama shi da shi na sayar da alburusan bindiga ba bisa ka’ida ba, a cewarsa shiga cikin damuwa ta rashi shine makasudin abin da ya jefa shi cikin wannnan hali.
Alhaji Ali Kwara, yace abin takaici ne ma cikin bata gari harda yan Banga da kuma maharban da suke taimakawa jami’an tsaro.
Domin Karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5