Ana dai ci gaba da gudanar da bincike don gano musabbabin hatsarin, wanda ya kifar da wani karagon jirgin gaba daya a saman wani karagon daya jirgin.
Jirgin, wanda ke dauke da tan 1,346 na tagulla, yana kuma cike makil ne da mutane, yayin da daya jirgin na da ma'aikata 10 a ciki da ke aikin gwajin saurin gudun jirgin, in ji kamfanin jirgin kasa.
Hukumomi ba su tantance mutanen biyu da aka kashe ba. Mutanen tara da suka jikkata sun hada da ‘yan kasar China hudu da ke karbar magani a asibitocin da ke kusa da wurin da hatsarin ya afku a San Bernardo na kasar Chile.
Ministan sufuri Juan Carlos Muñoz ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Associated Press cewa "Dole ne mu gano mene ne musabbabin hadarin kuma mu dauki matakan da suka dace."
-AP