Hadarin Hada Siyasa da Addini a Kasa Irin Najeriya

Shugaba Goodluck Jonathan

Masu kula da harkokin siyasa a Najeriya suna ganin shugaban kasar Goodluck Jonathan ya faye yin mahinman batutuwa a mijami'u kamar Kiristoci ne kawai suka zabeshi.
Ba'a hana shugabanni yin jawabi wurin ibada ba amma shugaban kasa ko ma wani dake shugabanci ya dauki harkar siyasa ya kai mijami'a ko masallaci babban kuskure ne musamman a kasa irin Najeriya wadda ta kunshi addinai da kabilu da yawa.

Idan aka cigaba da haka zai kawo rarrabuwan kawuna domin kwanakin baya an sha sukan shugaban kasa Jonathan sabili da kai abubuwan da suka shafi kasa mijai'a. Hakan ba daidai ba ne musamman ga kasa wadda bata dauki wani addini daya tamkar nata ba.Duk wanda ya kai maganar siyasa wurin ibada kamar yana neman mabiya wannan addinin su tausaya masa ne kuma ya nuna cewa shi nasu ne kawai. Yanzu babu yadda za'a ce shugaba Jonathan ya tafi Masallaci ko ba salla zai yi ba a ce ya yi irin maganganun da ya keyi a mijami'u.

Wanda shugaba Jonathan ya fara yi shi ne zancen Boko Haram. A mijami'a ya ce Boko Haram suna cikin gwamnatinsa. Dalili ke nan mutane suna tambaya ko yana son ya mayarda mulkinsa mijami'a ne. Da zai mayarda martani kan wasikar da tsohon shugaban kasa Obasanjo ya rubuta masa sai da ya je mijami'a ya yi. Yin hakan ya sa wasu suna tunanin yana neman ya jawo masu bin addinin Kirista su tausaya masa idan wata magana ta taso. Ana kokarin a kawar da hankulan mutane daga abubuwan dake damunsu su mayarda tunaninsu kan addini ko kabilanci.

Wadanda suke kawo addini ko Kiristanci ko Musulunci cikin harkokin siyasa suna da wata muguwar manufa daban. Misali yanzu shugaban yana son a mayarda wasikar da Obasanjo ya rubuta kamar takaddama ce tsakaninsu kawai babu abun da ya shafi kasar. Wannan kuma ba gaskiya ba ne. Shugaba Jonathan ya dauki wannan maganar ya kaita majami'a kamar ya gaza ne. Shugaba Jonathan ba zai iya fuskantar abubuwan da tsohon shugaba Obasanjo ya ambata ba a wasikar da ya rubuta masa, abun da ya sa ya yi babbar gazawa.

Ya kamata shugaba ya tunkari harakar addini daban da na siyasa daban. Idan ya yi haka zai iya yin shugabanci nagari yadda kowa ma zai daukeshi shugaban kwarai kuma shugaban kowa ne.

Ga karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Hadarin Hada Siyasa da Addini a Kasa Irin Najeriya