A wani mummunan hatsari da ya afku a safiyar Laraba, 16 ga Oktoba, 2024, wata tankar mai da ta fashe a garin Majiya da ke karamar hukumar Taura a jihar Jigawa, ta yi sanadin mutuwar mutane 94 tare da jikkata wasu 50.
Lamarin ya faru ne lokacin da wata tankar mai da ta taso daga Kano zuwa Yobe ta rasa yadda za ta yi, ta kife a kusa da jami'ar Khadija da misalin karfe 12:30 na safe.
A cewar rahotannin ‘yan sanda, fashewar ta tashi ne a lokacin da mazauna yankin suka garzaya wurin da abin ya faru, inda aka zarge su da yunkuri domin dibar man fetur din da ya zube.
Gobarar da ta tashi ta lakume dandazon jama’a, lamarin da ya kai ga wata mummunar gobara da ta kashe akasari a nan take.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Jigawa, DSP Lawan Adam ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya jaddada cewa dukkan wadanda abin ya shafa sun samu munanan raunuka.
Jami’an agajin gaggawa sun kai wadanda suka jikkata izuwa manyan asibitocin Ringim da Hadejia, inda suke samun kulawa.
Hukumomin yankin tare da hadin gwiwar al’ummar yankin sun fara jana’izar wadanda suka mutu.
Shaidu sun bayyana munin lamarin a matsayin rudani, inda jama’a suka yi kaca-kaca da kokarin tserewa daga wutar da ke ci gaba da yaduwa.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Jigawa, AT Abdullahi, ya jajantawa iyalan wadanda lamarin ya shafa, inda ya ce, “wannan rashi ce mara misaltuwa ga daukacin jihar. Tunaninmu da addu'o'inmu suna tare da iyalan wadanda suka mutu da kuma wadanda ke asibitoci suna fafutukar ceto rayukansu."
Tuni dai hukumomin kasar suka kaddamar da gangamin wayar da kan jama’a, inda suka bukaci jama’a da su kai rahoto ga hukumomin da abin ya shafa, tare da kaucewa taruwa a wuraren da ke zubar da mai, saboda yawaitar fashe-fashe.
Yanzu haka ana kokarin kai daukin gaggawa ga iyalan wadanda abin ya shafa, yayin da gwamnatin jihar ta yi alkawarin sake duba matakan tsaro a kan manyan tituna domin hana afkuwar irin wadannan hadurran nan gaba.
~Yusuf A. Yusuf