Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Akalla Mutane 40 Suka Mutu Sakamakon Fashewar Tankar Mai A Laberiya


Tankar Mai
Tankar Mai

Akalla mutane 40 ne suka mutu sakamakon fashewar wata tankar iskar gas a Arewa ta tsakiyar kasar Laberiya, a cewar babban jami'in kula da lafiya na kasar ta yammacin Afirka, Francis Kateh, a ranar Laraba.

WASHINGTON, D. C. - Tankar man ta yi hatsari ne da yammacin ranar Talata a Totota da ke karamar hukumar Lower Bong, kuma jim kadan bayan nan ta fashe, lamarin da ya yi sanadiyyar rasa rayuka da jikkata wasu da dama wadanda suka yi tururuwa zuwa wurin.

Mutane da dama ne ke kwance a asibiti sakamakon konewa, kuma adadin wadanda suka mutu na iya karuwa, kamar yadda Kateh ya shaida wa manema labarai.

Rashin kyawun hanyoyin mota da raunin ababen more rayuwa sun sanya yankin na kudu da hamadar Sahara ya zama yankin da ya fi muni a duniya wajen hadurra, inda adadin wadanda ke mutuwa ya ninka na Turai sau uku, a cewar alkaluman Majalisar Dinkin Duniya.

-Reuters

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG