Hadin Gwiwa Domin Inganta Hanyoyin Sadarwa Wajan Kai Daukin Gaggawa

A ci gaba da kokarin tabbatar da samar da intacciyar hanyar sadarwa domin mayar da martanin kai daukin gaggawa akan lokaci da hukumar kiyaye hadurra ta kasa FRSC ke yi, Marshal Boboye Oyeyemi ya kai ziyara a ma’aikatar sadarwa ta Nageriya domin kara karfafa hadin gwiwa tsakanin kungiyoyin biyu.

Wannan na daga cikin al'amurran da suka tattauna a lokacin da yake ganawa da Babban mataimakin shugaban ma’aikatar sadarwa ta kasa NCC, Farfesa Umar Garba Danbatta a shalkwatar hukumar dake Abuja, a cewar taron manema labarai da mai Magana da yawun hukumar Bisi Kazeem, ya jagoranta.

Mujallar Daily Post ta wallafa cewa babban jami’an hukumar kiyaye hadurran a bayanin da ya gabatar gaban mambobin hukumar, ya yaba da goyon bayan da hukumar ma’aikatar sadarwar ta basu a kokarinsu na neman ingantattun na’urorin sadarwa da zasu taimaka wajan sadarwa tsakanin ma’aikatan hukumar da al’umma a duk lokacin da suke bukatar taimakon kai daukin gaggawa.